Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jami'an Tsaro Da Na Kiwon Lafiya Sun Kada Kuri'unsu a Zaben Ghana


Jami’an da ke muhimman ayyuka a Ghana, ciki har da ‘yan sanda, ma’aikatan lafiya da sojoji sun kada kuri’unsu ranar Talata 1 ga watan Disamba gabanin babban zaben kasar da ke tafe ranar Litinin mai zuwa.

Shugaba Nana Akufo Addo na fafatawa da ‘yan takara 11, ciki har da tsohon shugaban Ghana John Mahama. Ana sa ran madugun ‘yan adawar ne zai zama babban dan hamayya a zaben kasar da ke yammacin Afrika.

Wata kafar yada labarai da ke Congo mai suna AfricaNews, ta ambaci wani binciken jin ra’ayoyin jama’a da cibiyar raya dimokrayya ta gudanar kwanan nan da ya nuna shugaba Akufo-Addo ke gaban Mahama da kadan. Batun farfado da tattalin arzikin Ghana ne muhimmin abu da dukkan ‘yan takarar biyu ke maida hankali a kai a yakin neman zabensu.

Hukumar zaben kasar Ghana ta ce za a sanya wakilan sa ido kan cutar COVID-19 a duk rumfunan zabe 311 na kasar don tabbatar da cewa masu kada kuri’a sun kiyaye matakan kariya, ciki har da sanya kyallen rufe hanci da baki, an kuma gwada zafin jikinsu sun kuma tsaftace hannuwansu.

Ghana ta tabbatar da samun sama da mutun 51,600 da suka kamu da coronavirus da kuma mace-mace 323, a cewar cibiyar jami’ar Johns Hopkin da ke bin diddigin annobar COVID-19 a fadin duniya.

XS
SM
MD
LG