Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaitattun Tarihin Manyan 'Yan Takarar Zaben Shugaban Kasa A Ghana


Manyan 'yan takara a Ghana, shugaba Nana Akufo Addo da tsohon shugaba John Mahama
Manyan 'yan takara a Ghana, shugaba Nana Akufo Addo da tsohon shugaba John Mahama

Kasar Ghana ta koma mulkin farar hula ne a shekarar 1992, yayin da ta gudanar da zaben raba gardama a kan kawo karshen mulkin soji bayan ta kwashe kusan shekaru 23 karkashin mulkin sojan.

Tsohon shugaba marigayi Jerry John Rawlings shi ne shugaban farko a jamhuriya ta hudu kana sai tsohon Shugaba John Agyekum Kuffour. Ghana ta sake zabo marigayi John Evans Atta-Mills, wanda ya rasu a kan gadon mulki, sa’annan Jiohn Dramani Mahama ya zama shugaba na hudu a jamhuriya ta hudu. Shugaban kasa mai ci yanzu Nana Akufo Addo, shi ne shugaba na biyar a jamhuriya ta hudu.

Karo na takwas kenan da Ghana zata yi zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisa a yau Litimin bakwai ga watan Disamban shekarar 2020, inda za a fafata tsakanin ‘yan takara 12, ciki har da shugaban kasa Nana Addo Dankwa Akufo Addo na jami’iyyar NPP mai mulki da John Dramani Mahama tsohon shugaban kasa na babbar jami’iyyar adawa ta NDC.

Manyan ‘yan takaran sun hada ne da shugaban kasa Nana Addo Dankwa Akufo Addo na jami’iyar NPP mai mulki, wanda aka haife shi a ranar 29 ga watan Maris din shekarar 1944 a birnin Accra.

Akufo Addo ya yi karatu a jami’ar Ghana Legon kana ya ci gaba da karatunsa a New College a Ingila da kuma jami’ar Landan, A baya ya rike mukamin babban lauyan gwamnati kana ya zama ministan harkokin wajen Ghana a karkashin mulkin tsohon shugaba John Agyekum Kufuor.

Ya yi takarar shugaban kasa sau biyu kafin ya lashe zabe a karo na uku tare da mai dafa masa baya Dr. Mahmud Bawumia mataimakin shugaban kasa da suke takara tare a karo na hudu.

Sai kuma John Dramani Mahama, tsohon shugaban kasar Ghana, wanda aka haife shi ranar 29 ga watan Nuwamban shekarar 1958 a garin Damango da ke arewacin Ghana.

John Mahama ya rike mukaman siyasa da dama, kama daga dan majalisa, karamin minister, babban minister, mataimakin shugaban kasa, kana ya zama shugaban kasa mai riko, inda ya karasa ragowar watanni shida na wa’adin marigayi shugaba John Evans Atta Mills. Daga bisani ya yi takara ya lashe zaben shugaban kasa a shekarar 2012.

John Mahama ya yi karatu a Institute of Social Sciences kana ya je jami’ar Ghana.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG