Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN NIGER: Manufofin Jam'iyyar MNSD Daga Bakin Ibrahim Tampone


MNSD Nasara, Niger Republic
MNSD Nasara, Niger Republic

Yau saura kawana 11 a yi zabe a kasar Nijer, kuma yanzu haka yakin neman zabe ya kankama dan haka ne shirin yau da gobe shirin matasa ya sami tattaunawa da Ibrahim Tampone mataimakin daraktan yakin neman zaben dan takarar jam'iyyar MNSD Nasara Seini Oumarou.

Wadanne manufofi wannan jam'iyya ta MNSD Nasara ta sa a gaba? ga amsar da Tampone ya bada;

"Manufofin wannan jam'iyya guda bakwai ne, da farko akwai karfafa mulkin demokaradiyya da bin dokokin kasa.

Na biyu shine neman 'yancin kai domin ciyar da kasa da inganta ayyukan gargajiya da noma da kiwo.

Na uku shine ba kowanne dan kasa cin moriyar kasa.

Na hudu kuma shine bunkasa arzikin kasa kamar su uranium da zinari da sauransu.

Na biyar shine tabbatar da tafiyar da kasa ta fuskar tattalin arziki da amfani da kudaden da val'uma take samu.

Na shidda kuma bunkasa sufuri da yawon bude ido.

Na bakwai kuma shine mayar da hankali akan bunkasa tafiyar da huldodin siyasa akan iyli, matasa ta wajan ayyukan motsa jiki da al'adu.

Wadannan sune manufofin da jam'iyyar tamu kuma da yardar Allah zamu faiyace komi da komi domin ganewa jama'ar kasar Nijer".

Saurari cikakkiyar hirar a nan.

  • 16x9 Image

    Ibrahim Jarmai

    Ibrahim Jarmai, ma’aikacin jarida (International Broadcaster Multi Media) a sashen Hausa na muryar Amurka, mai gabatar da shirye shirye a radio da talabijin, da kuma shafukan yanar gizo, dan asalin jihar Kasina.

XS
SM
MD
LG