Wani tsohon kwach na Super Eagles a Najeriya, Cif Adegboye Onigbinde, ya caccaki Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya, NFF, saboda abinda ya kira raina kurwar ‘yan Najeriya ta hanyar nada Sunday Oliseh, mutumin da bai taba koyar da wata kungiya ba, a zaman kwach na kungiyar ta kasa baki daya.
Onigbinde, wanda ya jagoranci Super Eagles zuwa gasar cin kofin kwallon kafar duniya ta 2002 a kasashen KOriya da Japan, ya ja kunnen hukumar ta NFF tun kafin wannan nadin na Oliseh mai shekaru 41 da haihuwa, inda har yace abin kunya ne ga hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta je tana rokon wani mutumin da bai taba koyarwa yazo ya koyar da ‘yan Super Eagles.
Cif Onigbinde, yace Oliseh ya fadawa duniya cewa shi bai roki a nada shi ba, watau dai hukumar kwallon kafa ke nan ta je ta durkusa ta roke shi. Wai shin me ta gani a jikinsa har da zata roke shi ya zo ya koyar da ‘yan wasa na kasa? In ji shi.
Tsohon kwach din na Super Eagles yace, shi a ganinsa, raina kurwar ‘yan Najeriya ne a je waje, ko kuma a cikin gida ma a dauki wani mutumin da bai taba koyar da wani kulob ba, bai taba jagorantar babbar kungiya ba, a ce za a damka masa jagorancin Super Eagles. Wannan ai cin zarafi ne, in ji Onigbinde.
Ya ci gaba da cewa, “Shin ‘yan Najeriya sun manta da yadda ‘yan Super Eagles suka wargaje baki daya suka ba Najeriya kunya a kasar Mali ne a lokacin da Oliseh yake kyaftin na kungiyar, saboda rashin biyayya? Amma ayanzu irin wannan mutumin ne hukumar NFF ta ga ya dace ta dauko ta damkawa kungiyar?.