Wani jirgin ruwa na ‘yan yawon shakatawa mai suna “Royal Caribbean Ship” Ya hadu da wata jarabawa. Shi dai wannan jirgin na daya daga cikin sabbabi kuma mafi girman jirgin ruwa a fadin duniya. A ranar Lahadi da ta gabata ne, jirgin na dauke da mutane 4,180, wata iska mai tsananin sanyi da karfi ta fuskanci jirgin, jim kadan bayan jirgin ya tashi daga tashar jiragen ruwa na jihar New York, zuwa Canavera a jihar Florida.
Cikin gaggawa matukin jirgin "Capting" ya umurci mutane 'yan yawon shakatawa dake cikin jirgin, da su koma cikin dakunan su, domin wannan iskar na iyayin barna, duk dai da cewar ansamu asarar dukiyoyi. Amma ba’a samu koda jimuwa ba ga fasinjojin. Isakar ta taso ne cikin bazata, don basu taba tunanin taba.
Tuni dai wasu fasinjojin suka fara rubuce-rubuce a shafufukan su na yanar gizo, don bayyana ma iyalansu irin halin da suke ciki. Ita dai irin wannan iskar takan kada jirgi, domin kuwa tana da matukar karfi kuma ga sanyi, hakan na iyasa jirgin ya kasa motsawa wanda sanadiyar hakan zai sa ya nitse cikin ruwa.