Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Gwamna A Jihar Anambra


Wata rumfar zabe a jihar Anambra (Facebook/ INEC)
Wata rumfar zabe a jihar Anambra (Facebook/ INEC)

Babu dai wani rahoto da ya nuna cewa an samu wata tangarda ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, illa ‘yar matsalar na’ura da aka samu a wasu rumfunan zabe a sassan jihar.

Rahotanni daga jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya na cewa jama’a sun yi tururuwa zuwa rumfunan zabe domin zabar gwamnan da zai mulki jihar cikin shekaru hudu masu zuwa.

Wa’adin mulkin Gwamna Willie Obiano ya zo karshe yayin da yake shirin kammala wa’adin mulkinsa na biyu.

Akalla jam’iyyu 18 ne suka fitar da ‘yan takarar da suke fafatawa a wannan zabe, wanda ya dauki hankalin jama’a da dama sassan Najeriya.

Rumfar zabe a Anambra (Facebook/INEC)
Rumfar zabe a Anambra (Facebook/INEC)

Bayanai sun yi nuni da cewa tun misalin karfe 8 aka bude rumfunan zaben, kuma tuni jama’ar da suka kama layi suke ta jefa kuri’unsu.

Babu dai wani rahoto da ya nuna cewa an samu wata tangarda ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, illa ‘yar tangardar na’ura da aka samu a wasu rumfunan zabe a sassan jihar.

A baya an zargi kungiyar IPOB mai fafutukar kafa kasar Biafra da shirin hana gudanar da zaben, batun kungiyar ta musanta.

Ana tantance mai kada kuri'a (Facebook/INEC)
Ana tantance mai kada kuri'a (Facebook/INEC)

Ko da yake, ta yi kiran a zauna a gida a lokacin zaben, amma daga baya ta janye kiran bayan abin da ta kira shawara da wasu shugabannin suka ba ta.

Bisa binciken da Muryar Amurka ta yi, ga gaggan ‘yan takarar da jama’a suke ganin za su fi fafatawa a zaben:

1. Ifeanyi Ubah – Young Progressive Party (YPP)

2. Valentine Ozigbo – Peoples Democratic Party (PDP)

3. Godwin Maduka – Accord Party

4. Akachukwu Nwankpo – African Democratic Congress

5. Andy Uba – All Progressives Congress (APC)

6. All Progressive Grand Alliance – Chukwuma Soludo

7. Obiora Dikeora – Zenith Labour Party

XS
SM
MD
LG