Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Yiwuwar Mu Saka Dokar Ta-Baci A Anambra – Malami


Ministan Shari'a Abubakar Malami (Facebook/Abubakar Malami)
Ministan Shari'a Abubakar Malami (Facebook/Abubakar Malami)

A ranar 6 ga watan Nuwamba hukumar INEC take shirin gudanar da zaben gwamna a jihar ta Anambra wacce ke kudu maso gabashin Najeriya.

Gwamnatin Najeriya ta ce akwai yiwuwar ta ayyana dokar ta-baci a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin kasar.

Babba Atoni janar din kasar kuma ministan Shari’a Abubakar Malami ne ya bayyanawa manema labarai hakan a ranar Laraba bayan kammala taron majalisar zartarwar kasar da aka saba yi na mako-mako.

Malami ya ce dole ne gwamnati ta tashi tsaye wajen kare lafiya da dukiyoyin jama’a yana mai cewa, a duk lokacin da gwamnatin jihar ta gaza aiwatar da hakan, ya zama hakki akan gwamnatin tarayya ta dauki mataki.

“Idan aka yi wa tsaron kasarmu barazana kuma muka lura cewa ana barazana ga tsarin mulkin dimokradiyya da dokar kasa ta amince da shi, za mu iya daukan kowane irin mataki.” Malami ya fadawa manema labarai a Abuja.

Jihar ta Anambra na shirin yin zaben gwamna a watan Nuwamba mai zuwa a daidai lokacin da masu fafutukar kafa kasar Biafra ke ta da zaune tsaye, ko da yake sukan nesanta kansu da wasu hare-haren da aka ke kai wa a yankin.

Yayin wani taron gaggawa da hukumar zabe ta INEC ta gudanar a Abuja, shugaban hukumar Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi gargadin cewa tashe-tashen hankulan da ke faruwa na masu hankoron ballewa a yankin, wata babbar barazana ce ga shirin gudanar da zaben na Anmabra.

Akan haka shugaban na INEC ya yi kiran da a samar da isasshen tsaro a wurare fiye da 6,000 da jami’ai fiye da 26,000 da za’a tura su gudanar da zaben a jihar.

Gabanin kalaman na Malami, mai bai wa shugaban kasa shawara kan lamurran tsaro Babagana Munguno, ya ba da tabbacin samar da cikakken tsaro a lokacin gudanar da zaben na jihar ta Anambra.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG