Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Gwamnan Jihar Anambra Na Fuskantar Barazana - INEC


INEC
INEC

"Rahotannin da hukumar ke samu na nuni da cewa babbar manufar wasu ‘yan ta da kayar baya, shi ne hana gudanar da zaben gwamnan jihar ta Anambra ko ta halin yaya."

Hukumar Zaben Najeriya, INEC, ta bayyana cewa shirin gudanar da zaben gwamna a jihar Anambra da ke kudancin kasar na fuskantar barazana.

An tsara gudanar da zaben na gwamnan jihar ta Anambra ne a ranar 6 ga watan Nuwamban nan mai zuwa.

To sai dai a yayin wani taron gaggawa da hukumar ta INEC ta gudanar a Abuja, shugaban hukumar Farfesa Nuhu Yakubu, ya yi gargadin cewa tashe-tashen hankalin da ke faruwa na masu hankoron ballewa a yankin, wata babbar barazana ce ga gudanar da zaben.

Ya bayyana cewa rahotannin da hukumar ke samu na nuni da cewa “babbar manufar wasu ‘yan ta da kayar baya, shi ne hana gudanar da zaben gwamnan jihar ta Anambra ko ta halin yaya.”

Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu (Instagram/inecnigeria)
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu (Instagram/inecnigeria)

Farfesa Yakubu ya ce babbar damuwar hukumar shi ne tsaron lafiya da rayukan jama’a masu jefa kuri’a, jami’an hukumar, da ma’aikatan ta na wuccin gadi da za su gudanar da zaben, da kuma jami’an tsaro, da su ma ke fuskantar hare-haren ‘yan ta da kayar bayan.

Akan haka shugaban na INEC ya yi kiran da a samar da isasshen tsaro a wurare fiye da 6,000 da jami’ai fiye da 26,000 da za’a tura su gudanar da zaben a jihar.

To sai dai kuma mai bai wa shugaban kasa shawara kan lamurran tsaro Babagana Munguno, ya ba da tabbacin samar da cikakken tsaro a lokacin gudanar da zaben a jihar ta Anambra.

Ana ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro a yankin kudu maso gabas, ciki har da jihar ta Anambra, sakamakon ayukan ‘yan kungiyar IPOB masu hankoron kafa kasar Biyafara, wadanda suka kara ta’azzara tun sa’adda aka kama jagoransu Nnamdi Kanu.

Wannan yanayi ya takaita ayukan gangamin yakin neman zabe a jihar da ke tunkarar zaben gwamna, a yayin da kuma ake fargabar yiwuwar kai hare-hare kan masu jefa kuri’a, jami’an zabe da kuma masu sanya ido kan gudanar da zaben.

XS
SM
MD
LG