Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Baiwa Jihohi N108B Domin Shawo Kan Matsalolin Amabaliya, Zaizayar Kasa


Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ne ya bayyana hakan a jiya laraba a fadar shugaban Najeriya dake Abuja.

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya amince da naira biliyan 108 ga jihohin Najeriya 36 domin su shawo kan matsalar ambaliyar ruwa da sauran nau’ukan bala’o’i.

Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ne ya bayyana hakan a jiya laraba a fadar shugaban Najeriya dake Abuja.

Da yake karbar bakuncin Kakakin Majalisar Wakilan Kasar, Abbas Tajudeen, mataimakin shugaban kasar ya bayyana halin da ake ciki a birnin Maiduguri da “iftila’in kasa baki daya”.

“Shugaban kasa ya nuna aniya da jajircewa ta yin hadin gwiwa da jihohi domin shawo kan wadannan matsaloli,” a cewar Kashim Shettima.

“A baya-bayan nan, ya amince da sakin naira biliyan uku-uku ga ilahirin jihohin kasar nan domin shawo kan wasu daga cikin wadannan matsaloli domin kowane sashe ya ji cewa ana tafiya tare.”

A nasa bangaren, Abbas Tajuddeen ya jajantawa Shettima da Tinubu da gwamnati da al’ummar jihar Borno, inda ya bada tabbacin cewa majalisun tarayya zasu samar da tallafi ga al’ummomin da ambaliyar ta shafa.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG