Su dai wadanda suka fice, sun yi zargin cewa rashin adalci da kama karya da kuma babakere su suka sa suka fice, zargin da shugabanin jam’iyar ke musantawa.
Daya daga cikin wadanda suka bar jam'iyyar, Mista Peter Achagwa, yace kafin daukar wannan matakin, sai da suka tuntubi magoya bayansu kusan dubu ashirin da tara wadanda yace dasu ne suka fice suka bar APC.
Mista Achagwa yace “duk inda ba za'a yi gaskiya ba, ba laifi bane idan ka bar wurin saboda haka muma mun hanga zabubukan da za’a yi na shuwagabanin jamiyar ba adalci, yanzu da nike gayamaka sun riga sun san waye ne chairman a wannan ward da local government mu bamu sani ba don ba’a yi zabe ba.”
Shugaban riko na jam'iyyar APC a jihar Taraba Alhaji Hassan Jika, cewa yayi Allah ya raka taki gona. Ya kara da cewa ”Mutane dubu nawa da suka fada din na karya ne. Idan akwai mutanen a kawo su mu gansu muna tabatar maku wanna lissafin mu sai mun baku sama da haka din yanzu wadanda suke da niyyan dawowa wanna jamiyar tunda wadanna munafikan sun fita."