Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zaben Amurka: Yadda Harris, Trump Suka Tafka Muhawara


Yadda mutane suka kalli muhawarar Trump da Harris a birnin New York a ranar 10 ga watan Satumbar 2024.
Yadda mutane suka kalli muhawarar Trump da Harris a birnin New York a ranar 10 ga watan Satumbar 2024.

'Yan takarar biyu sun yi musabaha a farko, suka tsaya a bayan mimbarinsu a wani dandamali a Cibiyar Kundin Tsarin Mulkin Kasa da ke Philadelphia, sannan suka fara caccakar juna.

Mataimakiyar Shugaban Amurka daga jam'iyyar Democrat, Kamala Harris, da tsohon shugaban kasa na jam'iyyar Republican, Donald Trump, ba su taɓa haɗuwa ba har sai a muhawarar shugabancin kasa da suka yi a daren Talata.

'Yan takarar biyu sun yi musabaha a farko, suka tsaya a bayan mimbarinsu a wani dandamali a Cibiyar Kundin Tsarin Mulkin Kasa da ke Philadelphia, sannan suka fara caccakar juna.

Sun yi takaddama kan tattalin arzikin Amurka, hakkin mata Amurkawa na zubar da ciki, batun shige da fice a kan iyakar Amurka da Mexico, yakin Isra’ila da mayakan Hamas a Gaza, mamayar Rasha a Ukraine, da rikicin ranar 6 ga watan Janairu, 2021 a Majalisar Dokoki yayin da ake tabbatar da cewa Trump ya sha kaye a zaben 2020.

Harris ta ambaci zaben 2020 da Trump ya sha kaye ga Shugaba Joe Biden, ta ce, "An sallami Donald Trump daga aiki da kuri'un mutane miliyan 81. Yana da wahalar fahimtar hakan."

Trump kwanan nan ya ce ya sha kaye a zaben "da ‘yar kankanuwar tazara," amma a dandamalin muhawarar ranar Talata, ya ce kalamansa na wancan lokacin barkwanci ne kawai kuma ya ki amincewa da ingancin sakamakon zaben 2020.

Sun tsaya kusan kusa da juna, suna girgiza kawunansu kan kalaman juna, inda Harris ta kusan yin dariya sosai kan wasu daga cikin bayanan Trump.

Masu gabatar da shirin na ABC News, David Muir da Linsey Davis, sun yi kokarin sarrafa tafiyar tattaunawar, amma wasu lokutan sun gaza yin hakan.

Miliyoyin Amurkawa ne suka kali wannan muhawara da watakila za ta kasance daya tilo a wannan lokacin yakin neman zabe.

Wannan fafatawar ta kasance makonni takwas kafin ranar 5 ga watan Nuwamba da za a yi zabe amma saura ‘yan kwanaki kadan kuma kafin fara zaben a wasu jihohi 50 na kasar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG