Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Miliyoyin Amurkawa Sun Shirya Tsaf Don Kallon Muhawarar Harris Da Trump


Trump, hagu da Harris, dama
Trump, hagu da Harris, dama

Kiyasi ya nuna mutum miliyan 51.3 ne suka kalli muhawarar Trump da Biden a watan Yuni, ana kuma hasashen wadanda za su kalli ta Trump da Harris za su haura wannan adadi.

Miliyoyin Amurkawa ne za su zauna a gaban akwatunan talabijin dinsu don kallon muhawarar Mataimakiyar Shugaban Amurka Kamala Harris ta jam’iyyar Democrat da abokin hamayyata na Republican tsohon Shugaban Amurka Donald Trump.

A wannan Talata za a fafata a muhawarar watanni biyu bayan muhawarar da aka yi tsakanin Trump da Shugaba Joe Biden – kafin ya janye takararsa ya mika ragama ga Harris.

Kiyasi ya nuna mutum miliyan 51.3 ne suka kalli muhawarar Trump da Biden a watan Yuni.

Ana kuma hasashen wadanda za su kalli wannan muhawara wacce za a yi a birnin Philadelphia na jihar Pennsylvania za su haura hakan duba da shaukin da jama’a ke nuna.

Sashen da manema labarai za su zauna a lokacin muhawarar wacce gidan talabijin na ABC zai jagoranta
Sashen da manema labarai za su zauna a lokacin muhawarar wacce gidan talabijin na ABC zai jagoranta

Kamala Harris da Donald Trump suna shiri daban-daban game da muhawarar neman shugabancin kasar, wanda ke nuna bambance-bambancen hangen nesansu ga kasar, da kuma yadda suke kimtsawa muhawarar.

Harris ta shafe karshen mako a kulle a wani tsohon otel a tsakiyar garin Pittsburgh, inda ta mai da hankali kan inganta yadda za ta ba da amsa cikin tsawon minti biyu kamar yadda ka'idodin muhawarar suka tanada.

A gefe guda kuma, Trump ya yi watsi da muhimmancin yin nazari don muhawarar a fili. Tsohon shugaban kasar ya zaɓbi cike kwanakinsa da ayyukan da suka shafi kamfen maimakon yin nazari.

Gidan talabijin na ABC ne zai jagoranci muhawarar.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG