Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muhawarar Mataimakan 'Yan Takarar Shugaban Kasar Amurka


Mike Pence da Kamala Harris
Mike Pence da Kamala Harris

Muhawara da aka tafka tsakanin mataimakan 'Yan takarar Shugaban kasar Amurka da ta kasance daya tilo da zasu yi kafin zaben shugaban kasa, ta tabo batutuwa da dama da suke sosawa Amurka rai.

Annobar coronavirus da ke ci gaba da addabar Amurkawa ce mabudin muhawarar tsakanin mataimakan ‘yan takarar shugaban kasar, a daidai lokacin da zauren muhawarar ya yi fatan alheri da samun sauki ga shugaba Donald Trump da uwargidansa da yanzu haka suke fama da cutar.

To sai dai dukkan mataimakan sun yi kokarin kariyar bayanan da masu gidajensu suka yi a muhawarar makon jiya, inda Kamala Harris ta jam’iyyar Democrats, ta kara jaddada cewa kasawar gwamnati mai ci yanzu, da kuma rashin ingantaccen tsarin tunkarar annobar, shi ne ya kara uzzura lahanin da cutar take yi a Amurka.

Ta ce “sakamakon halayyar wannan gwamnati na kin gayawa Amurkawa gaskiya, ya sa jama’a da dama sun ji jiki dalilin kasawar wannan gwamnati. Shin idan har ba’a fito an gayawa jama’a gaskiya ba ta yaya za su shirya har su dauki matakan kare kan su?”

Muhawarar Zaben 2020 a Amurka
Muhawarar Zaben 2020 a Amurka

To sai dai mataimakin shugaban kasa Mike Pence, wanda kuma shi ne ma shugaban kwamitin shugaban kasa na yaki da cutar COVID-19, ya ce damuwar da shugaba Trump yake da ita na kula da lafiyar Amurkawa, ta sa gwamnati daukar kwararan matakai tare da hadin gwiwar masana, domin ganin karshen wannan annobar.

Pence ya ce yanzu haka kamfanonin 5 na Amurka na dab da fitar da riga-kafin cutar a zaman wani sashe na kokarin gwamnati, to amma kuma ya bayyana damuwa, tare da zargin ‘yan takarar na Democrats da yunkurin bata kokarin na gwamnati, ta hanyar cirewa Amurkawa kwarin gwiwar karban riga kafin.

Ya ce “Gaskiya Magana shi ne kun ci gaba da kokari cirewa Amurkawa kwarin gwiwar amincewa da riga kafin, idan har aka sami riga kafin a lokacin mulkin Trump ina ganin babban ci gaba ne. ku daina sa siyasa ga abin da ya shafi rayukan jama’a. yadda kuke kokarin bata riga kafin a idon jama’a sam ba abu ne da za’a lamincewa ba.”

Kamala Harris da Mike Pence
Kamala Harris da Mike Pence

A bangaren tattalin arziki kuma, mataimakin shugaban kasa Pence ya ce gwamnatinsu ta yi hobbasa wajen bunkasa tattalin arziki, tare da samar da ayyukan yi ga Amurkawa, ya kara da cewa duk da yake annobar coronavirus ta yi illa ga nasarorin da suka samu, to amma kuma yanzu haka suna da tsari tare da kudurin sake farfado da tattalin arziki, ba kamar na jam’iyyar Demokrat da suka sha alwashin kara haraji ga ‘yan kasa ba.

To sai dai a martanin da ta mayar, Sanata Harris ta musanta wannan zargin, inda ita kuma ta zargi gwamnatin Trump da wargaza tattalin arzikin Amurka tare da rasa dimbin ayyukan yi, kazalika da soke abinda ta kira kwakkwaran shirin inshoran kiwon lafiya da suka gada daga gwamnatin Obama, lamarin da ta ce sun tsara gaggauta kawo dauki idan aka zabe su akan mulki.

yan-takarar-shugaban-kasar-amurka-sun-tafka-muhawara

trump-da-biden-sun-yi-musayar-zafafan-kalamai-a-muhawararsu

wasu-amurkawa-sun-fara-jefa-kuri-unsu

Wani muhimmin batu da aka tabo a muhawarar, shi ne dangantakar Amurka da China, da kuma irin tasirin da lamarin ke haifarwa ga Amurka.

Duk da yake dukkan masu muhawarar 2 sun ki su amsa kai tsaye, tambaya akan matsayin kasar China ga Amurka, to amma mataimakin shugaba Pence ya ce Amurka ba ta amfana da komai a danganta da China ba, a lokaci daya kuma ya ce Chinar ce ke da alhakin mawuyacin halin da Amurka ta ke ciki na annobar COVID-19.

Yace “China da Hukumar Lafiya ta Duniya – WHO sun ki gayawa Amurkawa ainihin gaskiya, sun hana jami’an mu shiga domin samun sahihan bayanai akan cutar coronavirus har zuwa tsakiyar watan Fabrairu. Nan take shugaba Trump ya haramta shige da fice da China amma Joe Biden fitowa yayi karara ya soki wannan mataki.”

To sai dai Sanata Harris ta zargi rashin samun alfanu a dangantaka da China, da yadda shugaba Trump yake tunkarar al’amuran da suka shafi kasashen waje.

Ta ce “Yakin kasuwanci, kamar yadda suka kira shi da ake yi da China, shi ne yayi sanadiyyar rasa ayukan yi kusan dubu 300 da suka danganci kamfanoni, yayin da Amurkawa kuma suke kashe makudan kudade domin samun kayayyaki saboda wannan yakin da ba nasara.”

Muhawar Shugaba Donald Trump tsohon Mataimakin shugaban kasa Joe Biden
Muhawar Shugaba Donald Trump tsohon Mataimakin shugaban kasa Joe Biden

Haka ma an tabo wasu muhimman al’amura da dama, akasari wadanda tuni an tattauna su a muhawarar farko, da suka hada da sauyin yanayi, sha’anin wariyar launin fata da kuma yiwuwar karbar sakamakon zabe, inda ‘yan takarar mataimakin shugaban 2 duk suka goyi bayan matsayar masu gidajen nasu a muhawarar farko.

Duk da yake dai mataimakan 2 sun caccaki juna a muhawarar, tare da yiwa juna katsalandan jefi-jefi, to amma kuma sabanin waccan ta farko a makon jiya, wannan muhawarar ta gudana cikin tsanaki, tare da mutuntawa da kuma girmama juna.

Saurari rahoton Murtala Faruk Sanyinna cikin sauti:

Muhawarar Mataimakan 'Yan Takarar Shugaban Kasar Amurka-3:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG