Kungiyoyin rajin mulkin Democradiya da shugabanci na gari da wasu 'yan Nigeria suna ci gaba da nuna damuwa kan yadda yan siyasa a kasar suke keta ka'idar yarjejeniyar kaucewa lafuzan tarzomar zabe, wadda yan takarar shugabancin Nigeria suka sanyawa hannu a Abuja, baban birnin taraiyar Nigeria kimamin watani biyu da suka shige.
Ana ci gaba da nuna damuwa akan yadda wasu 'yan takara da magoya bayansu suke karya alkawarin da suka yi cewa, zasu kaucewa fadan duk abinda zai hadasa tarzoma wajen yakin neman zabe.
Comrade Magaji, shugaban kungiyar Grassroot and Awareness yace irin abubuwan da suke faruwa a yanzu, za'a ga mutane da yan siyasa suna fitowa suna fadin magana yanda suke so. Kuma hukumomin tsaro ba zasu taba daukan wani mataki ba. Wannan na nuni da cewa yarjejeniyar da aka kula na kaucewa lafuzan tarzoma soki burutsu ne kawai.