Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN2015: Sakon Obama Ga 'Yan Najeriya


Shugaba Barack Obama.
Shugaba Barack Obama.

Yayin da ya rage kwanakin kadan 'yan Najeriya su je rumfunan zabe domin kada kuri'unsu, Shugaba Barack Obama ya yi kira da 'yan kasar da su tabbatar an gudanar da zabe na gari.

Shugaban Amurka Barack Obama ya yi kira ga ‘yan najeriya da su gudanar da zabe na gari yayin da kasar ke tunkara manyan zabuka a wannan asabar mai zuwa.

Mr. Obama ya kuma yi kira ga ‘yan kasar da su kaucewa rikici irin wanda ya gurbata zabukan da kasar ta yi a baya.

A wani faifan bidiyo da ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ya fitar, Mr Obama y ace zabe na gari na daga cikin matakan da za su iya kawo karshen kungiyar Boko Haram, wanda hakan zai baiwa ‘yan gudun hijra komawa muhallansu.

“Ina kira ga dukkanin shugabannin da ‘yan takara su gayawa magoya bayansu cewa tashin hankali bashi da hurumi a tsarin dimokradiya, kuma su tabbatar da cewa ba za su saka kansu akan wani abu da ya shafi rikici kafin zabe da lokaci zabe da bayan zabe.”

Ya kuma kara kira ga ‘yan Najeriya da su yi amfani da wannan dama su hada kai su yi biris da masu kiran a ta da hankali.

“Idan aka yi zabe lami lafiya, hurumin kowa da kowa ne ya ga cewa an zauna lafiya koda wanene ya ci zaben.” In ji Obama.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan zai yi takarar sake neman shugabancin kasar ne da Janar Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC.

A zaben shekarar 2011, rikici ya barki a wasu sassan kasar bayan da aka yi zargin cewa an yi magudin zabe yayin da ‘yan takarar biyu suka nemi shugabancin kasar.

XS
SM
MD
LG