Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2015: Kotu Ta Dakatar da Yunkurin Hana Janar Buhari Tsayawa Takara


Janar Muhammad Buhari na jam'iyyar APC
Janar Muhammad Buhari na jam'iyyar APC

Yayinda zaben Najeriya ke karatowa wata kotu ta dakile yunkurin hana Janar Buhari tsayawa takarar shugaban kasa.

Wadanda suka shigar da karar suna kalubalantar Janar Buhari ne akan wai bai kammala karatun sakandare ba domin bashi da takardar shaida.

Kotun tayi watsi da bukatar a tsayar da Buharin amma tace zata cigaba da sauraran karar ranar 23 na watan Afirilu, makonni uku bayan zaben shugaban kasa.

Abun tambaya nan shi ne yaya 'yan Najeriya suka dauki hukuncin. Wakilin Muryar Amurka ya zanta da wasu a Abuja domin jin ra'ayoyinsu. Wani Mustapha Malunfashi yace tun farko dai karar bata bisa tsari. Matsayin kotun ya nuna shari'a ta fara farfadowa a kasar.

Shi ma Abba Suleiman Gumel yace hukuncin kotun yayi dede. Alkalai sun yi anfani da hankulansu sun yi abun da zai dawo da darajar shari'a a Najeriya. Wani Abraham Sule yace hukuncin alkalin yayi dede domin karar ta tayarwa miliyoyin 'yan Najeriya hankali sabili da ana ganin wadanda suka kai karar suna da wata manufa ta daban.

A bangaren jam'iyyar PDP mukaddashin daraktan yada labarai na kemfen din shugaba Jonathan Isa Tafida Mafindi yace su kan ko a jikinsu. Duk da wai ba jam'iyyarsu ba ce ta shigar da karar Mafindi yace duk abun da shari'a tayi sun karba kuma sun yadda.

Tun farko jam'iyyar APC tace karar ta dauke hankulan 'yan Najeriya ne daga matsalolin da suka addabesu.

Ga rahoton Ibrahim Alfa Ahmed.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG