Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

ZABEN 2015: Matar Shugaba Jonathan Ta Kira Mata Su Zabi Mijinta


Matar Shugaban Najeriya Patience Jonathan.
Matar Shugaban Najeriya Patience Jonathan.

Uwargidan shugaban kasar Najeriya ta kai yakin neman zabe a Ibadan fadar gwamnatin jihar Oyo.

Patience Jonathan, yayin da take kemfen a Ibadan ta bukaci jama'ar jihar musamman mata su zabi mijinta zanar Asabar mai zuwa.

Matar shugaban tace tana son matan Najeriya, matan jihar Oyo da maza da matasa da yara su sani cewa akwai tanadi da gwamnatin mijinta tayi masu. Gwamnatin tayi masu tanadi a fannonin ilimi da aikin gona da samar da aikin yi da kuma bada tallafi. Tace kuma gwamnatin ita ce dake da tunanen matasa ko yara a zuci. Sabili da haka ya kamata a zabeta domin inganta rayuwarsu.

Matar shugaban, Patience Jonathan ta kara da cewa gwamnatin mijinta ta gyara hanyoyin Ibadan zuwa Ilori da Legas. Tayi kuma tanadi a harkokin kiwon lafiya da ma wasu. Patience ta yabawa matan jihar domin zaman lafiya lamarin da tace ya taimaka wurin bunkasa dimokradiya.

A nata jawabin mai kula da harkokin zaben shugaban a kudu maso yammacin Najeriya ministar kasa Jumoke Akinjide ta bukaci jama'ar jihar Oyo da su fito su zabi shugaba Jonathan a zaben ranar 28 ga watan Marin din nan.

Ga rahoton Hassan Umaru Tambuwal

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG