Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Kano Ta Shigar Da Sabbin Tuhume-Tuhume Akan Ganduje


Tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje (Facebook/Gwamnatin Kano)
Tsohon Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje (Facebook/Gwamnatin Kano)

Gwamnatin Kano ta shigar da sabbin tuhume-tuhume akan tsohon gwamnan jihar kuma shugaban jam’iyar apc na kasa mai ci, Dr. Abdullahi Ganduje.

A cikin takardar tuhumar da aka shigar a yau Talata, gwamnatin jihar ta zargi ganduje da tsohon Kwamishinan Shari’a, Musa Lawan, da hada baki domin aikata laifi da wawure kudade, laifuffukan da suka sabawa sashe na 308, kuma aka tanadi hukuncinsu karkashin sashe na 309 na kundin hukunta manyan laifuffuka da aka yiwa kwaskwarima, na kunshin dokokin jihar Kano dake tarayyar Najeriya.

Sabbin tuhume-tuhumen sun zayyano zarge-zargen almundahana da suka kunshi makudan kudade.

A cewar takardar tuhumar, ana zargin Ganduje da Lawan da hada baki domin wawurewa da karkatarwa harma da sauya Naira miliyan 240.

Takardar ta cigaba da bayyana cewar bangaren masu kara na shirin gabatar da shedu guda 4 domin bada shaida akan wadanda ake tuhuma.

Ta kuma zargi Ganduje, da yin amfani da matsayinsa na gwamna, wajen hada baki da Lawan, wanda ya rubuta takardar neman fidda kudade da zimmar gudanar da shari’o’in al’umma, da suka shafi ma’aikatan gwamnatin jihar Kano da ake zargin Hukumar EFCC ta ci zarafinsu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG