Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Tayi Watsi Da Karar APC Kan Neman Tsige Ganduje Daga Shugabancinta


Dr Abdullahi Umar Ganduje
Dr Abdullahi Umar Ganduje

Alkalin ya kori karar da wata kungiyar mambobin APC daga shiyar arewa maso tsakiyar Najeriya suka shigar a bisa la’akari da dimbin dalilai.

Mai Shari’a Ekwo ya bada hujjar cewar kungiyar ba mutum ko kamfani bace dake da hurumi ko rijista a shari’ance don haka ba ta da damar shigar da karar.

Alkalin ya kara da cewa masu karar sun gaza yin amfani da matakan sasantawa na cikin jam’iyya gabanin su garzaya kotu.

Ya ci gaba da cewa nadin mukaman da kwamitin zartarwar jam’iyyar APC ke yi wani al’amari ne na cikin jam’iyya wanda kotu bat a da hurumin tsoma baki a ciki.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG