Abin da ke nuna hakan shi ne yadda gwamnan Sakkwato Aminu Waziri Tambuwal ya yi kuskuren wani hari da aka kaiwa ayarin sa, bayan dawowa daga yekuwar neman zabe.
Ko bayan kwamitin da ke karkashin tsohon shugaban Najeriya Abdulsalam Abubakar wanda ke hada ‘yan siyasa wuri daya su saka hannu ga yarjejeniyar zaman lafiya a lokutan gudanar da lamurran su na siyasa, wasu hukumomi na gudanar da irin wannan aikin, kamar yadda rundunar ‘yan sanda ta yi a shekarar da ta gabata kafin a soma yakin neman zabe a Najeriya.
A yayinda suke hada jam'iyun siyasa wuri daya akan wannan manufar, kwamishinan ‘yan sanda a jihar Sakkwato, Muhammad Usaini Gumel, ya ce dukan su sun yi alkawalin gudanar da lamurran su cikin lumana, sai dai bayan soma yekuwar neman zaben lamarin ya fara sauyawa inda wasu da ake tuhumar ‘yan bangar siyasa ne suka tari ayarin gwamnan Sakkwato bayan dawowa daga yekuwar neman zabe.
Gwamnan wanda ke tare da dan takarar gwamna na PDP na jihar Kebbi sun samu tsira daga wannan harin, sai dai wasu dake cikin ayarin sun sha ruwan duwatsu.
Gwamnan ya yi tsokaci akan wannan harin inda ya ce gwamnati ba zata rungume hannu tana kallon irin wannan na gudana ba.
Shima kwamishinan yada labarai na jihar Sakkwato Akibu Dalhatu ya bayyana cewa tuni an kama daya daga cikin wadanda ake tuhuma da kai harin.
Murya Amurka ta kuma tuntubi kakakin jam'iyar adawa ta APC Sambo Bello Danchadi, sai dai ya turo rubutaccen sako wanda ya nisanta jam'iyar sa ta APC daga wannan aika-aika wadda ya ce bata cikin koyarwar jam'iyar a jihar.
Masu sharhi akan lamurran yau da kullum irin farfesa Bello Bada na ganin cewa ba yarjejeniyar sa hannu ne kawai ya kamata a rika shiryawa ‘yan siyasa ba har da hukunta masu kunnen kashi.
Yanzu dai da yake akwai sauran kusan wata biyu kafin zabe matakin da mahukunta zasu dauka akan irin wannan matsalar kan iya nuna ko za'a magance ta ko akasin haka.
Saurari rahoton a sauti: