Kotun da ke sauraren korafe-korafen zabe a jihar Osun da ke kudu maso yammacin Najeriya ta ayyana Adegboyega Oyetola na jam’iyyar APC a matsayin asalin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta INEC a Najeriya ta ayyana Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben wanda aka yi a ranar 16 ga watan Yulin bara.
Sai dai a hukuncin da ya yanke, Alkali Tetsea Kume da ya jagoranci tawagar alkalan kotun, ya ce an yi arangizon kuri’u a zaben.
Hakan ya sa kotun ta soke kuri’un da aka kada na boge, abin da ya sa kuri’un Oyetola suka karu zuwa 314, 921 yayin da na Adeleke suka ragu zuwa 290, 266.
A halin da ake ciki, kotun ta ba INEC umarni da ta janye takardar lashe zabe da ta ba Adeleke ta ba Oyetola.
Oyetola ya kasance gwamna mai ci a zaben, inda yake neman wa’adi na biyu.
A watan Agustan bara, Oyetola da jam’iyyarsa ta APC, suka kalubalanci nasarar Adeleke a kotun da ke sauraren korafe-korafen zabe a jihar.