Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bobrisky: Verydarkman Ya Bayyana Gaban Majalisar Wakilai Kan Zargin Almundahana Ga EFCC


Bobrisky
Bobrisky

A yau Litinin, dan jaridar intanet Martins Otse da aka fi sani da Verydarkman ya gabatar da kansa gaban kwamitin majalisar wakilai mai binciken zargin cin hanci da rashawa da ake yiwa jami’an hukumar yaki da almundahana ta Najeriya (EFCC) da takwararta mai kula da gidajen gyaran hali (NCS)

Bugu da kari, jami’an hukumomin EFCC dana ncos suma suna wurin sa’ilin da kwamitocin majalisar wakilan Najeriya akan laifuffukan da suka shafi kudi da gyaran hali suka fara gudanar da bincike game da zarge-zargen cin hanci da rashawa da dan jaridar yake yiwa hukumomin efcc dana gyaran halin.

A wani faifan bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, Verydarkman ya yi zargin cewar shahararen dan daudun nan mai yawan jawo cece-kuce, Idris Okuneye, da aka fisani da Bobrisky ya biya jami’an EFCC Naira miliyan 15 domin su yi watsi da tuhumar da suke yi masa ta cin zarafin Naira a watan Afrilun da ya gabata wanda bayan haka ne wata kotu ta yanke masa hukuncin zaman gidan kaso na watanni 6.

Dan jaridar intanet din ya kuma yi zargin cewa Bobrisky ya biya miliyoyin nairori domin samun wurin alfarma a kurkuku.

Tuni dai Baobrisky ya musanta wadannan zarge-zarge yayin da hukumomin EFCC da NCOS suka umarci a gudanar da bincike a kan zargin da dan jaridar ke yi.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG