Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EFCC Ta Mika wa NELFUND Naira Biliyan 50


Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) Ola Olukoyede
Shugaban Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) Ola Olukoyede

“Wannan kudi ba gudunmowa ba ne kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka ruwaito, kudi ne da hukumar ta kwato ta mika wa gwamnati."

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC a Najeriya ta mika wa asusun da ke ba da tallafin karatu na NELFUND Naira biliyan 50.

Cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Laraba, EFCC ta ce kudin na daga cikin kudaden da aka kwato daga masu yi wa tattalin arzikin kasar zagon kasa.

“Wannan kudi ba gudunmowa ba ne kamar yadda wasu kafafen yada labarai suka ruwaito, kudi ne da hukumar ta kwato ta mika wa gwamnati.

“A kokarinsa na kai wag a marasa galihu, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yanke shawarar a saka kudaden a asusun bai wa dalibai bashi.” Sanarwar ta EFCC ta ce.

“Ba hurumin hukumar ta EFCC ba ne ta yanke shawarar inda gwamnati za ta zuba wadannan kudade da aka kwato.” Sanarwar ta kara da cewa.

Ya zuwa yanzu NELFUND ya tantance jami'o'in, kwaleji-kwaleji da sauran manyan makarantu a matakin jiha sama da 100 da za a fara ba dalibansu bashin karatu.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG