A Jamhuriyar Nijer shugabannin hukumar zabe ta CENI, sun gana da shuwagabannin jam’iyyun siyasar kasar, game da shirye-shiryen zabubbukan da ake saran gudanarwa a shekarar 2020 da 2021.
Hakan na faruwa ne yayin da ‘yan adawa ke ci gaba da kauracewa ayyukan wannan hukuma da suke yi wa kallon maras cikakken halacci.
Shugaban hukumar zabe ta CENI, mai shari’a Issaka Sounna, ya yi wa wakilan jam’iyyun siyasa bayani a dangane da tsare-tsaren babban zaben kasar ta Nijar, inda ya sanar cewa komai ya kankama game da batun rajistar sunayen mutanen da suka cancanci kada kuri’a, saboda haka za’a soma wannan aiki daga ranar 1 ga watan Oktoba.
Malan Nafiou Wada shi ne kakakin wannan hukuma, ya ce sabanin yadda hukumar ta bayyana a can baya, cewa za’a soma zaben a ranar 1 ga watan November 2020, za’a gudanar da zaben kansiloli, sannan zaben ‘yan majalisar dokoki hade da na zagayen farko na zaben shugaban kasa, a ranar 27 ga watan December 2020, kafin a cike da zagaye na 2 na shugaban kasa a ranar 21 ga watan Fabrairun 2021.
Soumana Mahamadou na jam’iyar PJD HAKIKA, ya ce, rashin halartar ‘yan adawa a al’amuran tsare-tsaren wadanan zabubbuka ya fara damun wasu ‘yan siyasar.
Hukumar ta CENI ta gayyato kamfanin da aka bai wa kwangilar hada kundin rajista domin ya yi bayani akan halin da ake ciki game da wannan aiki.
Ga rahoton Wakilin muryar Amurka a yamai, Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum