A cikin jawabinsa Frayim Ministan ya ce a cikin shekaru biyu da kamfanin ya soma kwangilar aikinsa bai kai kashi bakwai ba cikin dari duk da yawan jawo hankalin kamfanin da suka sha yi.Ya ce kawo yanzu ya kamata a ce aikin ya haura fiye da kashi arba'in cikin dari. To amma ba haka lamariin yake ba. Ya ce idan aka lura akwai gazawa da kayan aiki da dai makamantansu wanda hakan zai yi wuya a cimma dogon burin kasar ta Nijer idan aka bar kwangilar hannun kamfanin. Kwangilar ta kai kimanin sefa sama da miliyan dari hudu a yayin da aka ce ita gwamnatin Nijer bata baiwa kamfanin kudi fiye da kashi takwas cikin dari ba.
Kungiyoyin fararen hula a kasar sun yi murna da jin labarin. Sai dai sun ce ya kamata mahukuntar Nijer su yi hattara a kan yarjejeniyar, su san dabarar da zasu bi domin kamfanin ko kasar Rasha na iya kai kara a nahiyar turai.
Ga karin bayani na Abdullahi Mamman Ahmadu.