An bada sammacin kama lauyan da ke kare masu gonakin da matatar man kasar Nijer ta ratsa ta cikin su.
WASHINGTON, DC —
Wani babban alkalin kotun jahar Zinder ya bayar da sammacin kama Larwanou Abdourahamane, lauyan da ke kare masu gonakin da matatar man fetur ta bi ta cikin su a kasar Nijer, alkalin na neman lauya Larwanou ne bisa tuhumar shi da wani tsohon laifi mai nasaba da tonon sililin da ya yiwa wasu manya-manyan jami’an kasar Nijer da suka karbi “abun hasafi” da nufin kashe maganar biyan diyyar gonakin. Amma masu kare hakkokin bil Adama a kasar ta Nijer irin su malam Nouhou Arzika na ganin cewa sammacin wata barazana ce ta neman hana lauya Larwanou yin aikin shi na kwatarwa masu gonakin hakkin su. Karshen ta ma an dakatar da Larwanou Abdourahamane kamar yadda lauyan shi malam Oumarou Cisse ya tabbatarwa da wakilin Sashen Hausa a birnin Niamey Abdoulaye Mamane Amadou: