Hukumomin kasar jamahuriyar Nijer sun gana da 'yan kasuwa a wani kokarin neman karya farashin kayan matsarufi albarkacin watan azumin Ramadan
WASHINGTON, DC —
Hukumomin kasar jamahuriyar Nijer na ci gaba da tattaunawa da masyu saye da sayarwa da nufin sawwaka farashin kayayyakin matsarufi a wannan watan na Ramadana. Ministan kasuwancin kasar malam Saleye Saidou ya gana da manyan 'yan kasuwa da kuma kungiyoyin fararen hula masu yaki da tsadar rayuwa a wani kokarin neman karya farashin kayayyaki ko talaka ya samu sa'ida. Wakilin sashen Hausa a birnin Niamey, Abdoulaye Mamane Amadou ya halarci taron, ga rahoton da ya aiko ma na: