Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yobe: Wani Abun Fashewa Ya Tashi A Fitacciyar Kasuwar Dabbobi

Kasuwa sayar da dabbobi ta Apo da ke Abuja, Najeriya
Kasuwa sayar da dabbobi ta Apo da ke Abuja, Najeriya

Wani mazaunin garin Buni Yadin, Ali Hassan ya shaidawa tashar talabijin ta Channels ta wayar tarho cewar, al’amarin ya faru ne da misalin karfe 12 da rabi na ranar yau Juma’a, kuma ya raunata wata yarinya.

Wani abun fashewa da ake zargin bam din da aka birne ne ya tarwatse a fitacciyar kasuwar dabbobin nan ta Buni Yadi dake karamar hukumar Gujba ta jihar Yobe.

Wani mazaunin garin Buni Yadin, Ali Hassan ya shaidawa tashar talabijin ta Channels ta wayar tarho cewar, al’amarin ya faru ne da misalin karfe 12 da rabi na ranar yau Juma’a, kuma ya raunata wata yarinya.

Shima kakakin shiya ta 2 na aikin wanzar da zaman lafiya na hadin gwiwa mai taken “Operation Hadin Kai”, Kyaftin Muhammad Shehu ya tabbatar da afkuwar lamarin, inda ya ce sojoji sun yi nasarar gano wani bam din da aka birne a kasuwar tare da tarwatsa shi.

Ya kara da cewa mutum guda da fashewar ta shafa, na samun kulawa a daya daga cikin asibitocin da ke garin Buni Yadi.

Ya kuma jaddada cewa al’amarin ba harin kunar bakin wake bane illa kawai bam ne da aka birne a kasa.

Garin Buni Yadi mai tazarar kilomita 54 tsakaninsa da Damaturu babban birnin jihar, na cikin karamar hukuma a jihar da ta fi fama da ayyukan ta’addanci, inda ta kasance karkashin mayakan Boko Haram tsawon shekaru 2.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG