Da take maida martani game da hare-haren bam da aka kai a Karamar Hukumar Gwoza ta jihar Borno, Shelkwatar Tsaron Najeriya, ta bayyana cewa hare-haren na rikidewa zuwa yanayi na yaki.
Da yake sharhi game da munanan hare-haren, a sanarwar daya fitar, Daraktan yada labaran shelkwatar tsaron, Manjo Janar Edward Buba yace, “kasancewar muna cikin yanayi na yaki, wajibi ne a fahimci cewa wannan mumunan al’amari martani ne game da nasarorin da dakarunmu dake aikin wanzar da zaman lafiya suke samu.”
Ya kara da cewa, “hakika, ayyukanmu na baya-bayan nan sun hallaka jagororin ‘yan ta’addar tare da rage musu karfi, goyon baya da tasirin da suke dashi.”
Edward Buba ya bayyana cewar hare-haren bama-baman da aka kai sun hada da harin kunar bakin wake.
Ya cigaba da cewa, rundunar sojin kasar nan na kallon dukkanin rayukan da suka salwanta, na farar hula ko soja, matsayin mummunan bala’i.
“A madadin Babban Hafsan Saron Najeriya, Janar Christopher Musa, da sauran dakaru manya da kanana, muna mika sakon ta’aziyyarmu a daidai lokacin da muke alhinin rasa masoyanmu. Muna kuma mika sakon jaje ga wadanda ke bukatar waraka da farfadowa.”
Haka kuma, shelkwatar tsaron ta bukaci ‘yan Najeriya su hada kai tare da zama masu sanya idanu, sannan su ci gaba da baiwa kokarin Rundunar Sojin Najeriya goyon baya, harma da tabbatar da dorewar zaman lafiya da tsaron kasar a nan gaba.
A saurari rahoton Hassan Maina Kaina:
Dandalin Mu Tattauna