Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wani Harin Bam Ya Taba Shagon Shan Shayi A Mogadishu


Wadansu jami'an tsaro suna wucewa gaban shagon da aka kona a Mogadishu, Somalia, May, 8, 2017.
Wadansu jami'an tsaro suna wucewa gaban shagon da aka kona a Mogadishu, Somalia, May, 8, 2017.

‘Yan sanda sun ce an kashe mutane biyar wasu ashirin kuma sun jikkata a harin da aka kai birnin Mogadishu.

Wani mummunan harin bam na mota ya taba wani shagon shan shayi da kofi a tsakiyar birnin Mogadishu, a daidai lokacin da masu shan shayi ke kallon wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Turai ta 2024 tsakanin Ingila da Spain.

'Yan sanda a Mogadishu sun ce mutane biyar ne suka mutu yayin da wasu 20 suka jikkata a harin.

A wata sanarwa da rundunar ‘yan sandan ta fitar a shafinta na Facebook, ta tabbatar da cewa wata mota da aka dankarawa bama-bamai da aka ajiye a wajen shagon shan shayi na Top Cafe ce ta tashi.

‘Yan sandan sun ce bam din ya tashi ne da karfe 10:28 na dare agogon yankin.

Wani da ya tsira daga harin ya shaida wa kafafen yada labaran kasar cewa yana kallon wasan ne a cikin shagon a lokacin da fashewar ta faru.

Mutumin wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda dalilan tsoro, ya ce wadanda ke zaune a wajen shagon su harin ya fi shafa.

Harin dai na zuwa ne kwana daya bayan da jami'an tsaron Somaliya suka dakile wani yunkurin fasa gidan yari a babban birnin Mogadishu, bayan da wasu fursunoni 'yan bindiga suka yi amfani da bindigogin hannu da gurneti, suka far wa dogarawan da ke gadin gidan yarin.

Hukumomin kasar sun ce an kashe dogarawan da ke gadin gidan yarin uku, sannan an kashe fursunoni ‘yan bindiga biyar a harin na ranar Asabar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG