Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Babu Tsaro A Wasu Iyakokin Jihar Borno – Gwamnatin Jiha


Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zullum.
Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zullum.

A cewar kwamishinan, mai yiwuwa maharan sun yi amfani ne da kan iyakokin jihar da babu tsaro wajen kai hare-haren.

Gwamnatin jihar Borno ta bayyana kaduwarta dangane da harin bama-bamai da suka auku a yankin Gwoza na jihar wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da jikkata wasu da dama.

“Ba gazawa aka samu a fannin tattara bayanan sirri ba. Kuskure ne da ba mu hango ba,” Kwamishinan Yada Labarai da Tsaron Cikin Gida na Jihar Borno, Usman Tar ya ce a ranar Litinin a wani shiri na gidan talabijin na Channels Television, Sunrise Daily, kwanaki bayan fashewar abubuwa da yawa.

Mutane da dama ne suka mutu a jerin hare-haren bama-baman wanda daya daga cikin su ya faru a yayin wani bikin aure a jihar a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Hare-haren sun kuma jikkata wasu da dama a ranar Asabar da al’amarin ya faru, in ji hukumomin gaggawa.

A cewar kwamishinan, mai yiwuwa maharan sun yi amfani da kan iyakokin jihar da ba sa tsare wajen kai harin na bam.

“Idan ‘yan ta’adda suna son kai hari kuma suka yi amfani da wata hanyar da ba ku sani ba, me za ku iya yi? Kamar yadda ka sani iyakokinmu na waje ba a tsare suke ba.

Ya kara da cewa, “hatta kan iyakokinmu na cikin gida babu cikakken tsaro,” in ji Usman. “Idan ‘yan ta’adda na son kai hari, suna yin hakan ne ta hanyar amfani da sahun gaba. Wataƙila abin da ya faru ke nan.”

Sai dai wani shugaban al’umma a Borno Ayuba Bassa ya zargi gwamnati da jami’an tsaro da rashin yin wani abu da ya dace wajen magance ta’addanci. Ya ce akwai alamun irin wadannan hare-hare na zuwa amma ba a yi wani abu don dakile su ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG