Haka kuma, kwamitin yana hada kai da jami'an tsaro har ma da mafarautan gargajiya domin samo daliban da aka ce sun gudu cikin daji har yanzu ba su fito ba.
Shugaban kwamitin, Barrister Ahmed Mustapha, wanda shi ne kwamishinan shari'a na Jihar Yobe, ya ce kwamitinsu zai nazarci irin taimakon gaggawa da gwamnatin jihar zata iya bayarwa ga iyayen daliban da aka kashe da wadanda suka ji rauni. Haka kuma zasu dubi matakan da gwamnatin zata iya dauka na gaggawa domin taimakawa malaman makarantar da iyalansu.
Zasu kuma duba yadda zasu gyara abubuwan da aka lalata a makarantar.
Yace a wurin taronsu na farko jiya jumma'a, kwamitin ya yanke shawarar tuntubar jami'an tsaro da ku ma mutanen Sarkin Baka domin su binciko dajin dake kewaye da makarantar, musamman ma ta yamma da makarantar, inda aka yi imanin cewa akasarin dalibai sun gudu ta nan.