'Yan bangar sun nuna damuwar cewa wannan lamarin yana daukar wani sabon salo inda barayin dake tare hanya su na yin fashi suka canja salo, su ma su na shigar soja su na kai farmaki a kan garuruwa da bankuna da wuraren sana'o'in jama'a su na kwashe musu dukiyoyi ta hanyar fakewa da Boko Haram.
Jami'in hulda da jama'a na Kungiyar Vigilante ta 'yan bangar, Malam Mohammed Abbas Gaba, yace idan har gwamnati zata taimaka musu da kayan aiki, to su ma zasu bi sahun matasa 'yan bangar da aka fi sani da suna Civilian JTF ko 'Yan Gora, su shiga cikin dazuzzukan da wadannan 'yan bindiga suka buya domin zakulo su.
Kafofin labarai da dama sun bada rahotannin cewa a lokacin farmakin da aka kai kwanakin baya a kan garin Bama na Jijhar Borno, maharba na kungiyar 'yan Banga ta Jihar Borno, sun kai dauki tun ma kafin sojoji, inda aka ce sun kwace makamai tare da kashe wasu daga cikin 'yan bindigar da suka kai harin.