Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya Ce Kan Gaba Wajen Cin Hanci Da Rashawa


Taswirar Duniya inda Kungiyar Transparency mai yaki da zarmiya take nuna inda ake da matsalar a fadin Duniya.
Taswirar Duniya inda Kungiyar Transparency mai yaki da zarmiya take nuna inda ake da matsalar a fadin Duniya.

Alkaluma sun nuna cewa cin hanci da rashawa yayi katutu sosai a Najeriya, inda dubban miliyoyin nairori suke salwanta ba tare da bin bahasi ba.

Kungiyar yaki da zarmiya da cin hanci a duniya, Transparency International, ta ce a bana, matsalar ta kara yin muni a fadin duniya, musamman a kasashe masu tasowa.

Rahoton Mizanin Cin Hanci da Rashawa wanda kungiyar ta wallafa jiya talata ya nuna cewa har yanzu ba ta sake zani ba a Najeriya, inda ake ce an kashe kudade masu dimbin yawa a ayyukan gwamnati, amma kuma ba a ganin abubuwan da aka ce an yi da su.

Kungiyar ta ce a Najeriya, an yi hasarar Naira miliyan har sau miliyan biyu da wani abu da sunan tallafin farashin man fetur, sannan an ce an kashe Dalar Amurka fiye da miliyan dubu 20 a kokarin samar da wutar lantarki, ga shi har yanzu babu wutar.

Wani darekta a Cibiyar Bincike Kan Siyasa da Albarkatun Kasa a Najeriya, Buhari Bello Jega, yace a fili yake cewa shugabannin Najeriya ba su nuna sha'awa kan yaki da zarmiya da cin hanci ba. Yace an kafa kwamitoci masu yawan gaske da suka gano yadda ake satar kudi ta fitar hankali a Najeriya, amma har yanzu babu abinda shuga Goodluck Jonathan ya tabuka wajen maganin wannan abu.

Sai dai kuma mai ba shugaba Jonathan shawara kan harkokin siyasa, Ahmed Gulak, yace babu gwamnatin da ta kuduri yaki da cin hanci da rashawa kamar ta su, har ma yayi misali da yadda aka gurfanar da Bode George da tsohon sufeto-janar na 'yan sanda Tafa Balogun gaban kotu.

Ga cikakken rahoton Madina Dauda daga Abuja kan wannan bayanin.

Najeriya Ce Kan Gaba A Zarmiya Da Cin Hanci - 4:00
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:00 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG