Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Za'a Fara Taron Kasa da Kasa Akan Rikicin Syria


John Kerry, Sakataren harkokin wajen Amurka
John Kerry, Sakataren harkokin wajen Amurka

Yau Alhamis ake sa ran fara taro na share fage kan shawarwarin da za'a gudanar, da zummar kawo karshen rikicin da ake yi a Syria.

Gobe Jumma'a ce a hukumance za'a fara shawarwari ka'in da na'in a birnin Vienna, inda kasashen Rasha, da Turkiyya da Saudi Arabiya da Amurka. A karon farko Iran zata halarci taron kasa da kasa kan rikicin na Syria.

Sakataren harkokin wajen Amurka John kerry yace shawarwarin da za' a yi a Vienna gameda makomar Syria itace "dama mai hasken gaske" da aka samu cikin shekaru da suka wuce domin cimma maslaha ta fuskar siyasa gameda kasar da yaki ya dai-daita, wacce take cikin wahala da bashi misaltuwa cikin shekaru hudu da rabi d a suka wuce.

Mr. Kerry wanda ya bayyana haka a wani jawabi da ya gabatar a gidauniyar cibiyar mai aiki domin tabbatar da zaman lafiya ta kasa da kasa dake nan Washington jiya Laraba,yace Amurka tana aiki a kibla biyu kan rikicin na Syria.

A bangare daya zata nemi masalaha ta fuskar difilomasiyya. A gefe daya kuma zata ci gaba da gudanar da kamfen datake yi na yaki da kungiyar ISIS karkshin rundunar taron dangi da Amurka take yiwa jagoranci. Kerry yace rundunar zata kara baiwa 'yan tawayen Syria masu sassaucin ra'ayi taimakon kayan fada, tareda zafafa hare hare da take kaiwa da jiragen yaki, tareda kara matsin lamba kan kungiyar ta wajen kai farmaki kan helkwatarta dake birnin Raqqa.

Ana sa ran Mr.Kerry ya tashi zuwa Vienna bayan jawabin da ya gabatar.

Ahalinda ake ciki kuma,bayan watanni Amurka tana inda-inda kan matsayar da sojojin Amurka a Iraqi, kakakin ma'aikatar tsaronAmurka kanal Steve WQarren, ya fito karara yace sojojin Amurka suna fagen daga ne a yankin.

Tunda farko a wunin jiya Laraban, wakilan majalisar dokokin Amurka suna tambayar yadda za'a yi a sami ci gaba a shawarwarin da za'a yi a Vienna ganin akwai gibi kan matsayar Amurka kan rikicin na Syria, idan aka kwatanta da kasashen Iran da Rasha.

XS
SM
MD
LG