Shugaba Bashar al-Assad ya sake jadada niyarshi ta kakkabe barazanar ‘yan ta’adda a kasarsa, yace wannan ce hanyar da za a cimma matsayar siyasa da al’ummar kasar Syria suke hankoro da kawo karshen rikicin da kasar ta tsunduma a ciki na tsawon shekaru hudu da rabi.
Assad ya gana da wata tawagar ‘yan majalisar dokokin kasar Rasha da wadansu jami’ai a Damascus. Kamfanin dillancin labaran kasar SANA yace shugaban kasar ya jadada cewa kakkabe kungiyoyin ta’addancin zai kare diyaucin kasar Syria da kuma mutuncin yankinta.
Wani daga cikin tawagar kasar Rashan, dan majalisa Alexander Yushchenko yace Assad ya fada cewa, a shirye yake ya gudanar da sabon zaben shugaban kasa da na majalisa idan abinda al’ummar kasar Syria suke so ke nan.
Assad yana wani rukunin mulki na uku bayanda aka sake zabensa bara, ya shugabancin kasar na tsawon shekaru bakwai.An gudanar da zaben ne a yankunan dake karkashin ikon gwamnati kawai, zabenda kuma yan hamayya suka kauracewa. Assad ya sami kashi 89 bisa dari na kuri’un.