Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yawan Amurka Dake Zuwa Dakin Ganin Likita Na Gaggawa Ya Ragu Sosai: CDC


Wani rahoton cibiyar dakile yaduwar cuttuka ta Amurka ya ce zuwa dakin ganin likita na gaggawa da marasa lafiya daba na coronavirus ya yi kasa sosai a watan Afrilu a lokacin da annobar ta yi kamari.

Cibiyar ta fitar da hasashen a ranar Laraba cewa matsalar ta fi shafuwar yara ‘yan shekaru 14 da haihuwa da kasa da haka, da mata da kuma mutanan da suke zaune a yankin gabashin Amurka. Hukumar CDC ta lura da saukar adadin mutane da suke neman kulawar gaggawa da suke fama da ciwon kirji, ciki har da bugun zuciya tare da raguwar yaran da suke bukatar taimako akan rashin lafiyoyi kamar cutar Asthma.

Amurka take adadi mafi yawa da aka tabbatar sun kamu da COVID-19 sama da miliyan 1 da dubu dari 8, kuma wadanda suka mutu dubu 107 da 175.

Jaridar New York Times ta ba da rahoto cewa gwamnatin Trump ta zabi kamfanoni 5 da ake tsammanin za su samar da allurar rigakafi coronavirus. Kamfanonin su ne Moderna da ke jihar Massachusetts, da AstraZeneca wanda ya hada kai da jami’ar Oxford, da kuma babban kamfanin harhada magunguna na Jonhson & Jonhson da Merck da Pfizer.

Jaridar Times ta rawaito jami’an gwamnati suna cewa Fadar White House za ta sanar da matakin na ta nan da wasu makwanni kadan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG