Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sakataren Harkokin Tsaron Amurka Ba Ya Goyon Bayan Amfani Da Karfin Soji


Mike Esper
Mike Esper

Sakataren harkokin tsaron Amurka Mike Esper ya ce, ba ya goyon bayan yin amfani da karfin soji domin dakile zanga-zangar da ta karade kasar, kamar yadda Shugaban kasa Donald Trump yayi hasashe a farkon makon nan.

Da ya ke jawabi ga manema labarai a hukumar tsaron Amurka ta Pentagon a yau Laraba, Esper ya ce sam bai goyi bayan amfani da dokar matakin gaggawaba, wadda za ta baiwa Trump damar yin amfani da dakarun soji domin magance zanga-zangar da ake yi akan tituna, sakamakon mutuwar Goerge Floyd, ba’amurke bakar fata da ya rasa ransa a Hannun ‘yan sandan Minneapolis.

Esper ya ce “ana amfani da dokar ne kawai a matsayin zabi na karshe, kuma a yanayin matakan gaggawa kadai” wanda ya ce kuma ba’a kai ga shiga wannan yanayi ba a yanzu.

Haka kuma Esper yayi sharhi akan shigar sa hoton da shugaban kasa yayi a ranar Litinin, inda aka fatattaki masu zanga-zanga a kusa da fadar White House, inda ya ce sam bai da masaniya a wannan lokacin cewa za’a je daukan hoton ne.

Ya ci gaba da cewa yana kokari ya ga cewa ya nisanta ma’aikatar tsaro da sha’anin siyasa, to amma kuma ya ce sau da yawa baya samun nasara a wannan kokarin.

Sakataren na ma’aikatar tsaro ya kuma yi Allah waddai da matakin ‘yan sandan na Minneapolis da yayi sanadiyyar mutuwar George Floyd. Inda ya ce kuma yana fatan ganin an gudanar da zanga-zanga cikin lumana da za ta nuna karramawa ga marigayin, da kuma ci gaba da fafutukar neman adalci akan mutuwarsa, da fafutukar ganin an yaki wariyar launin fata a Amurka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG