Yayin da ake fama da matsalar tattalin arzikin da annobar coronavirus ta haifar da kuma zanga-zangar nuna bacin rai kan mutuwar bakar fata a hannun ‘yan sanda, masu kada kuri’a a jihohi takwas da babban birnin Washington DC, sun tsaya kan layi jiya Talata domin kada kuri’unsu a zaben da jam’iyya ke yi na fitar da ‘yan takarar Majalisar Wakilai da ta Dattawa.
Daya daga cikin zabukan da suka fi jan hankali shine na jihar Iowa, inda tsohon dan Majalisa mai ra’ayin mazan jiya Steve King ya sha kaye a hannun Randy Feenstra.
Shi dai King ya yi suna ne tun lokacin da aka zabe shi a karon farko a shekarar 2003 bisa ra’ayinsa kan zubar da ciki da kalaman nuna wariyar launin fata, musamman ma kan bakin haure.
Teresa Leger ta sami nasara kan Plame a kamfen dinta na neman tsayawa takarar Majalisar Wakilai a jihar New Mexico, wadda take zaman lauya mai kare ‘yancin al’umma.
Shi kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Joe Biden na ci gaba da kusantar zama dan takarar shugban kasa na jam’iyyar Democrat, bayan lashe zaben fidda dan takara a wasu jihohi masu yawa a jiya Talata. Biden ya kasance wanda ake sa ran zai zama dan takarar tun lokacin da ya lashe zaben jihar South Corolina a watan Fabarairu, bayan da ya samu goyon baya daga fitaccen bakar fatar Amurka Jim Clyburn.
Facebook Forum