Yaya Jameh wanda ya mulki kasar tasa na tsawon shekaru 22, ya fada a cikin jawabin da yayi wa ‘yan kasar ta kafar talabijin a ranar Talata, cewa ba abinda ya damu kasashen nan masu sa baki cikin batun zaben. Yace ya rage ga kasar ta shawo kan matsalar ta, nako ya mika mulki bayan kayen da yasha a cikin zaben watan Disamban bara.
Hari la yau shugaban yayi gargadi akan yada jita-jitan da ba ta da tushe tare da baza bayanan karya wanda zai iya zubar masa da kima.
Jammeh wanda ya fadi zaben da baiyi tsammani ba ga abokin karawarsa Adama Barrow a ranar daya ga watan Disambar bara, yakiya amince da sakamakon zaben a bisa hujjar cewa kasashen waje sune suka kara dama lissafi na yin katsalandan game da zaben.
Jammeh yace yayi imanin kasar ta Gambia na iya shawo kan matsalarta ba sai wata kasa ko kuma wasu kasashe sun yi mata shisshigi ba.
Da farko dai Jammeh ya amince da sakamakon zaben amma daga bisani kuma sai jam’iyyarsa ta kai kuka ga hukumar zabe, tana cewa an tafka magudi a zaben.
Can da, a ranar 10 ga wannan watan ne aka sa ran babban kotun kasar zata yanke hukunci game da wannan rigimarta zabe amma kuma yanzu ta dage zuwa watan Mayu, domin bata da tabbacin ko za ‘a mika mulki cikin ruwan sanyi ko kuma a’a.
A kan haka ne kasashen yammacin Africa suke kokarin ganin sun tattauna da Shugaba Jammeh domin ganin ko zai yarda ya sauka cikin ruwan sanyi.
Sai dai alamu sun nuna cewa Jammeh yana son ya dakata har sai abinda hukuncin kotu ta tabbatar kana ya amince ko kuma a’a.
Sai dai kuma idan ya tsaya akan wannan matsaya to ga bisa dukkan alamu zasu yi fito na fito dazababben shugaban Adama Barow wanda yace yana ci gaba da shirye-shiryen karban mulkin a ranar sha tara ga wannan watan da muke ciki.