Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hukumomin Nijar Sun Kama Wani Fitaccen Dan Jarida


Ousman Toudou
Ousman Toudou

A jamhuriyar Nijar kungiyoyin kare hakkin ‘yan jarida sun bayyana damuwa bayan da jami’an tsaron jandarma suka kama wani dan jarida, Ousman Toudou, mai rajin kare dimokradiya kuma mashawarcin tsofaffin shugabanin kasa Issouhou Mahamadou da Bazoum Mohamed.

Kawo yanzu ba a bayyana dalilan cafke wannan dan jarida ba koda yake wasu na hasashen cewa rubutun da ya yi a shafinsa na facebook a washegarin juyin mulkin 26 ga watan Yuli don nuna rashin jin dadi kan yadda sojojin Nijar suka yi kaurin suna wajen kifar da gwamnatin farar hula ne mafari.

Da yammacin Asabar din da ta gabata ne jami’an tsaron jandarma suka kama fitaccen dan jaridan Ousman Toudou suka kuma kai shi ofishinsu da ake kira Brigade de Recherche dake nan birnin Yamai. Lauyansa Hamed Maman da Muryar Amurka ta tuntuba ya tabbatar da faruwar wannan al’amari.

Kawo yanzu ba a bayyana dalilan kama wannan dan jarida ba wanda ya rike mukamin mashawarci kan harakokin sadarwa a zamanin tsohon shugaban kasa Issouhou Mahamadou aikin da ya ci gaba da gudanarwa a zamanin hambararren shugaban kasa Mohamed Bazoum.

Inji lauyansa wanda ya kara da cewa ya sami ganawa da shi kuma ba wata alamar damuwa a tattare da shi.

A washegarin juyin mulkin da sojoji suka yi wa shugaba Mohamed Bazoum dan jarida mai rajin kare dimokradiya Ousman Toudou, a rubutun da ya yi a shafinsa na facebook, ya nuna rashin jin dadinsa kan wannan al’amari da kusan ke neman zama wata al’ada a wajen sojojin Nijar.

Hasali ma hujojojin da suka bayar wajen kifar da gwamnati ba su da tushe inji shi abin da ya sa ake hasashen watakila wannan matsayi ne mafarin cafke shi.

Wannan ba shi ne karon farko da wani dan jarida ke fuskantar fushin hukumomi ba tun bayan juyin mulkin 26 ga watan Yuli, domin ko a watannin farkon faruwar wannan al’amari wasu mutane sanye da farin kaya sun dira gidan wata ‘yar jarida mai fafutika ta blog Samira Sabou suka yi awon gaba da ita kafin daga bisani ta bayyana a ma’aikatar tattara bayanan sirri. lokaci kadan bayan haka ministan cikin gida ya bada sanarwar dakatar da ayyukan gamayyar kungiyoyin ‘yan jairida ta kasa wato Maison de la Presse matakin da kungiyoyin kare hakkin ‘yan jarida ke kallonsa tamkar wani yunkurin rufe bakin manema labarai.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:52 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG