Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Take Ranar Tausayawa Bil Adama a Fadin Duniya


Majalisar Dinkin Duniya ta ware duk ranar 19 ga watan Agusta a matsayin ranar tausayawa Bil Adama a fadin Duniya.

Yayin da duniya take bukin ranar tausayawa bil’adama, MDD tana kira da a daina kaiwa farin kaya da masu ayyukan jinkai hari, wadanda suke sadaukar da rayukansu domin tallafawa maza da mata da kuma kananan yara da yaki ya rutsa da su.

Ranar sha tara ga watan Agusta rana ce da MDD tayi mummunan rashi. A ranar, cikin shekara ta dubu biyu da uku, aka kai harin bom a ofishin MDD dake Bagadaza babban birnin kasar Iraq, aka kashe jakadenta Sergio Vierra de Mello da kuma wadansu mutane ishirin da daya.

Shekaru biyar bayan aukuwar wannan lamarin, majalisar ta zartas da kudurin ayyana ranar goma sha tara ga watan Agusta ta kasance ranar da za a karrama ma’aikatan jinkai da suke sadaukar da rayukansu domin yiwa wadansu hidima.

Domin tunawa da wannan ranar, a bana, MDD tana jawo hankali kan kaiwa ma’aikatan lafiya da kuma cibiyoyin aikin jinya hari, da kuma illar hakan ga al’umma.

MDD tace an kai irin wadannan hare hare dari uku da biyu da suka janyo asarar rayukan mutane dari hudu da goma sha takwar bana, galili a kasar Syria.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG