Yayinda yake jawabi a taron koli kan tsaro da gwamnonin jihohin Najeriya da shugabanin hukumomin tsaro, Mukaddashin shugaban Najeriya Farfasa Yemi Osinbajo ya ce gwamnati ta damu da yadda kalamun batanci a yankunan kasar daban daban ke yaduwa.
Yana mai cewa gwamnati zata dauki batun da mahimmanci ta daukan kalamun batanci tamkar ayyukan ta'addanci. Injishi, gwamnati ba zata amince da kalamun batanci ko tunzurawa jama'a ba. Ya ce gwamnati za ta yi maganin masu kalamun batanci da take ji kullum daga bangarori daban daban na kasar. Makasudin kowace gwamnati shi ne wanzar da zaman lafiya da kare dukiyoyin jama'a, inji Osinbajo.
Farfasa Muhammad Tukur Baba kwararre akan kimiyar zamantakewar jama'a ya ce "Idan aka bar mutane suna ta maganganu kowa ya fadi abun da yake so, da mai dadi da mara dadi yana iya jawo wata babbar takaddama a gaba da ba za ta yiwa kowa dadi ba".
Farfasa Tukur yayi misali da abun da ya faru a kasar Rwanda can baya. Rikicin kashe kashen da aka yi ya fara ne da rashin fahimtar juna da kalamun batanci da maganganu na kiyayya har suka kai ga kashe junanasu.
Shi ma Dan Masanin Fika Alhaji Bababo Abba yace gwamnati kadai ba zata iya tayi maganin kalamun batanci ba. Kamata yayi a kira dattawa da shugabannin kasa da manya su yi magana kowa ya ji ya koyi daratsi.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Facebook Forum