Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Buhari Na Samun Sauki Sosai - Dogara


Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Yusuf Dogara
Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Yusuf Dogara

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya da takwaransa na Majalisar Dattawa sun ziyarci Shugaba Buhari a London sun tabbatar shugaban yana samun lafiya sosai

A sakonsa na shafin Twitter kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Yakubu Dogara yace ya gamsu da yadda Shugaba Buhari ke murmurewa daga rashin lafiyarsa.

Yakubu Dogara da takwaransa na Majalisar Dattawa Dr Bukola Saraki sun kai ziyarar ganin shugaban kasa London inda suka sadu dashi har suka yi fira ta kusan awa daya. Ya bukaci 'yan Najeriya su cigaba da yiwa shugaban addua tare da yin godiya saboda jin addu'o'in jama'a akan shugaban.

Inji kakakin "Godiya ta tabbata ga Allah Madaukakin Sarki wanda Ya sa suka ziyarci Shugaba Buhari a birnin London ...muka tattauna dashi na kusan sa'a daya. Na yi matukar farin cikin ganinsa cikin anashuwa da ba'a. Babu shakka Shugaba Buhari na samun lafiya sosai. Ina kira ga al'umma Najeriya da mu cigaba da bashi cikakken goyon baya..."

Kakakin yayi fatan Allah ya ba shugaban cikakken koshin lafiya ya kuma maidashi Najeriya lafiya.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:18 0:00

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG