Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta cafke wani limamin coci da ake zargi da cinikin yaran da aka sato a jihar, inda aka kuma zarge shi da yin amfani da su wajen yin tsafi.
Paston mai suna Samuel Babatunde wanda shi ke jagorantar cocin Cherubim and Seraphim Church da ke yankin Sango-Ota, ya shiga hannun ‘yan sanda ne bayan da aka zarge shi da sayen wasu yara biyu.
Masu bincike sun tono gawarwakin wani abu da ba tantance ko mene ne ba a cocin yayin da suka kai ziyara wajen ibadar.
Sai dai Pastor Babatunde ya musanta cewa gawar ta yaran ce, inda yayin ganawa da manema labarai da harshen yarbanci ya bayyana cewa gawar ta wasu aladu ne da ya binne domin nemar cocin kariya.
Amma mutumin da ake zargi da sato yaran, Jeremiah Ademola ya fadawa manema labarai cewa Pastor Babatunde ne ya sa shi ya kawo mai yaran, inda ya saye ko wane daya a farashin naira 50,000.
“A lokacin da mu ke bincike ya (Jeremiah) amince cewa shi kwararre ne a fannin satar yara kuma ya ce yana kaiwa wani malamin coci mai saka fararen tufafi, mun kuma tona wani bangare na cocin inda mu ke zaton kabari ne, an kwashe burbushin da aka gani a ciki za a gudanar da bincike.” In ji kwamishinan ‘yan sandan jihar Ogun, Ahmed Iliyasu.
Saurar rahoton Hassan Umaru Tambuwal domin jin karin bayani:
Facebook Forum