Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Kamaru Tace Mayakan Sa Kan Kasar Su Ajiye Makamai Ko Kuma....


Jami'an tsaron Kamaru
Jami'an tsaron Kamaru

Kasar Kamaru tace ta kafa wani kwamiti da zai raba daruruwar mayakan ‘yan awaren kasar da Boko Haram da makamai, wadndaa suka amince su ajiye makamansu kana a sake maida su ga jama’a.

Sai dai masu fashin baki sun ce kwamitin nada jan aiki a gabansa a yankin masu amfani da harshen Ingilishi, inda fadar tsakanin gwamnati da mayakan ‘yan awaren ke kara ta’azzara.

Tashin hankalin na zuwa ne kasa da mako daya bayan shugaba Paul Biya ya kafa kwamitin kasa da zai kwace makamai, ya wargaza kungiyoyin ta’addancin kuma ya maida ‘yan Boko Haram masu yaki a arewacin kasar da ma mayakan ‘yan aware dake arewa da kudu maso yammacin kasar da suka amince su ajiye makamai kuma a saka su cikin jama’a

Gwamnati tace an kafa wannan kwamiti ne domin taimakawa daruruwar tsofaffin mayakan sa kai da suka karbi kirar shugaba Biya da su ajiye makamai kuma a yi musu afuwa ko kuma su ci gaba da yaki sojoji su hallakasu

Kungiyoyin ‘yan bindgan dai suna fafutukar karbarwa yankin kasar mai amfani da harshen Ingilishi ‘yancin kai ne. Akasarin al’ummar Kamaru suna amfani na da harshen Faransanci.

Wannan yakin ‘yan awaren ya lakume sama da rayukan dubu daya da dari biyu, a cewar alkalluma da gwamnati ta fitar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG