Amurka ta sake bude offishin jakadancin ta a babban birnin Magadishu na kasar Somaliya, bayan ta kwashe shekaru da dama da rufe offishin.
Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka Heather Nauart, ta fitar da ke cewa an bude sabon offishin a ranar Lahadi.
Wannan abun tarihin yana nuna cewar kasar Somali na samu cigaba cikin ‘yan shekarun nan, hakan na kara kyautata dangantakar difilomasiyya tsakanin kasar da Amurka da ita a cewar sanarwar.
A hukunce Amurka ta yarda da sabuwar gwamnatin tarayyar kasar Somaliya a shekar 2013, amma duk da haka Amurka ta kebe wani karamin ofishinta a wani bangaren offishin jakadancin Amurka dake Nairo a kasar Kenya.
Tsohon jakadan Amurka Donald Yamamoto, ya isa birnin Mogadishu, a matsayin sabon jakadan Amurka a kasar Somaliya.
Facebook Forum