Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Ne Ake Bikin Ranar Ruwa Ta Duniya


Yau ranar Talata ne ake bikin ranar ruwa ta duniya da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe domin samar da ruwan shag a bil Adama, an dai kebe duk ranar 22 ga watan Maris na kowacce shekara domin wannan biki.

Najeriya ma tabi sahun sauran kasashen wajen dake gudanar da wannan biki ta yin taruka da bayyana muhimmancin ruwan sha mai tsafta. Hakan yasa wakilin Muryar Amurka dake jihar Lagos, Salihu Jibril, ya ji ta bakin wasu mazauna birnin da kuma gwamnatin jihar akan kokarin da suke na samar da ruwan sha.

Babban sakatare a hukumar samar da ruwan sha a jihar Lagos, Kabiru Ahmed Abdullahi, yace suna iya kokarinsu na ganin sun samar da ruwan sha, duk da yake abune mai kunshe da kalubale, amma ana tunkarar hanyar da za a samar.

A shekarar 1992 ne a wajen wani taron Majalisar Dinkin Duniya akan ingantar muhalli da kuma ci gaban kasa da aka gudanar a birnin Rio de Janeiro na kasar Brazil, aka ware wannan rana domin bukin ranar ruwa ta duniya.

Domin karin bayani saurari rahotan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG