Shugabannin Afurka za su hallara a birnin Accra na kasar Ghana a asabar din nan don shaida rantsuwar kama aiki na sabon shugaban Ghana Nana Akupo Addo, da zai karbi ragama daga shugaba mai barin gado John Dramani Mahama.
Bayan wannan rantsuwar shugabannin, karkashin jagorancin da ECOWAS ta dorawa shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, za su yi zama don daukar matakin warware takaddamar shugabancin Gambia inda shugaba Yahaya Jammeh ya ki amincewa da sauka daga mulki bayan Adama Barrow ya lashe zaben.
Matakin da shugabannin ka iya dauka zai iya kai wa ga matakin karfin soja kamar yadda tun farko kungiyar raya tattalin arzikin Afurka ta yamma Ecowas ta nuna alama.
Yahaya Jammeh dai ya yi watsi da barazanar ta Ecowas da nuna hakan tamkar kaddamar da yaki ne kan Gambia.
Jammeh wanda ya samu mara bayan rundunar sojan kasar, ya ce ba wanda ya isa ya tsorita shi kuma Allah ne`kadai zai iya sauke shi daga mulki.
Ga karin bayanin da mai taimakawa shugaban Najeriya kan labaru Garba Shehu ya yi