Maganar inganta ilimi da kyautata shi na cikin manufofin duka 'yan takarar shugabancin kasar jamhuriyar Nijer a zaben da za'a yi a kasar ranar 21 ga watan nan, saboda haka ne shirin yau da gobe ya tattauna akan ilimin kasar.
Kamar yadda shirin ya saba, yakan gayyaci shugabanni daga bangarori daban daban domin jin ta bakinsu musamman dangane da al'amurran da suka shafi matsaloli da kuma gyaran kasa.
Dan haka ne shirin ya gayyato ministan ilimin sakandire Mme Bety Aichatou, da kuma Soumana Sambo Ousseini babban magatakardar kungiyar daliban kasar Nijer ciki da waje inda shirin ya tattauna da su kai tsaye.
saurari cikakken shirin a shafin mu na voahausa.com kuma ana iya sauraren bayanan da magatakardar yayi a dandalinvoa.com
Danna nan domin saurare...